April 18, 2025

APC ta rufe hedkwatarta da ke Abuja.

Jam’iyyar APC mai mulki a ranar Alhamis ta sanar da rufe hedikwatar ta ta kasa da ke lamba 40, titin Blantyre Wuse 2, Abuja.

A cewar wata sanarwa da ke dauke da kwanan wata 10 ga watan Afrilu 2025, wacce Mataimakin Daraktan Gudanarwa na jam’iyyar Ubagba Abel ya sanya wa hannu, an rufe hedikwatar ne domin jimamin rasuwar Daraktan mulki na jam’iyyar Hon. Lateef AbdulRaif Adeniji.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace Adeniji kimanin watanni biyu da suka gabata a Abuja, kuma an kashe shi duk da cewa jam’iyyar ta biya kudin fansa naira miliyan 50 domin a sake shi.

Sanarwar mai taken “Rufe Hedikwata domin Jimamin Rasuwar Daraktan mulki” ta bukaci jami’an jam’iyyar da su yi amfani da lokacin da aka ware don yin addu’a ga iyalan sa da masoyan sa.

“Sakataren Jam’iyyar na Kasa ya amince da rufe Hedikwatar ta Kasa daga duk wasu ayyukan jam’iyya ko na ofis daga yanzu har zuwa Litinin, 14 ga watan Afrilu 2025.

“An yanke wannan hukunci ne bayan samun labarin rasuwar marigayi Hon. AbdulRaif Adekunle Adeniji, Daraktan mulki,” in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *