Siyasa
Trending

APCin Kano Na Son EFCC Ta Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Bello.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Jam’iyyar APC a jihar Kano, ta bukaci hukumar EFCC, da ta kaddamar da bincike kan abin da ta kira “badaƙala” ta baya-bayan nan da ta shafi kashe kuɗaɗen da ake zargin na kwangilar samar da magunguna ga kananan hukumomi 44 na jihar.

Hakan ya biyo bayan bidiyon da Ɗan Bello ya saki ne, wanda ake zargin ana yin abin da bai dace ba wajen siyen magunguna a ƙananan hukumomin, tare da kefe wani kamfani ana bashi kwangilar.

Tini dai gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayar da umarni a yi bincike kan lamarin ya na mai cewa bashi da masaniya kan batun.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button