Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar, ya nuna damuwa kan zargin cin zarafi, tsoratarwa, da rashin adalci da aka yi wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wanda Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta gabatar, ya bukaci a gudanar da “bincike mai zurfi, cikin adalci, kuma na gaskiya.”
A wani saƙo da ya wallafa a shafin sa na X, Atiku ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da Majalisar Dattawa da su ɗauki waɗannan zarge-zarge da muhimmanci ta hanyar tabbatar da “bincike na kwarai, na gaskiya.
Atiku ya ce, “Tunda yanzu akwai mata huɗu kacal a Majalisar Dattawa, dole ne mu samar da yanayi da zai ba su damar yin aiki ba tare da tsoro ko cin zarafi ba.”
“Wannan lokaci ana buƙatar ɗaukar mataki mai hikima da adalci domin kare mutuncin hukumomin mu da tabbatar da cewa kowane dan Najeriya ba tare da la’akari da jinsi ba, ya na samun mutunci da girmamawa.”
A cewar jagoran adawa, “waɗannan zarge-zarge suna da girma, don haka dole ne a gudanar da bincike mai zurfi, da adalci, kuma na gaskiya.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja