Daga Sani Ibrahim Maitaya
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar adawa ta PDP a zaben 2023 Atiku Abubakar, ya caccaki Shugaba Bola Tinubu kan yadda gwamnatin sa ke tafiyar da harkokin tsaro, yana mai cewa shugaban na rasa dabaru wajen shawo kan matsalar tsaro.
A wata sanarwa da Atiku ya wallafa a shafukan sa na sada zumunta da daddare ranar Assabar, ya ce gwamnatin yanzu ta nuna cikakken gazawa, rashin kwarewa, da kuma rashin wata ingantacciyar dabara wajen shawo kan matsalar tsaro da ke kara ta’azzara a Najeriya.
Atiku ya ce “Wannan ba ra’ayina kaɗai ba ne, yawancin shugabannin adawa, kwararrun masana tsaro da kuma wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar mai mulki, kodayake suna jin tsoron bayyana hakan a bainar jama’a, amma sun yarda da wannan gaskiyar a ɓoye.”
Ya ƙara da cewa jinin ‘yan Najeriya marassa laifi na ci gaba da zubewa ba kakkautawa, yana mai ambato kisan da aka yi kwanan nan a yankunan Logo da Gbagir na ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benue.
Ya kara da cewa “Duk da haka, gwamnatin Tinubu na nuna halin ko-in-kula, ba ta nuna gaggawa ko tausayi ga al’umma ba.
“Shugabanci na bukatar kasancewa a gaban jama’a. A shekarar 2016, Shugaba Barack Obama ya katse wata muhimmiyar ziyara ta diflomasiyya don komawa gida, bayan wani dan bindiga ya kashe jami’an ‘yan sanda biyar”.
“A 2019 Shugaba Cyril Ramaphosa ya fasa wata ziyara zuwa Masar don komawa Afirka ta Kudu, sakamakon matsalar wutar lantarki. Har ma Sanata Ted Cruz na Amurka, wanda aka caccaka bayan ya tafi zuwa Mexico a lokacin wani hadarin sanyi da ya kashe mutane a Texas, daga bisani ya dawo ya kuma amsa kuskuren sa,” in ji shi.
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasar ya bayyana cewa a 2014, tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya dawo daga ƙasar Equatorial Guinea, bayan wani fashewar bam a Abuja.
“Wannan shi ne mafi ƙarancin abin da ake tsammani a irin waɗannan lokutan na bala’in ƙasa.
“Amma Shugaba Bola Tinubu, wanda ya gaza shawo kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, yana yawo a Turai kamar yana mulkar Najeriya daga hutu.
“Idan ba zai iya yin aiki ba, mafi ƙarancin abin da zai iya yi shi ne bayyana a bainar jama’a. Idan ba zai iya shugabanci da tausayi ba, to ya yi ƙoƙarin nuna hakan. Najeriya na zubar da jini. ‘Yan Najeriya na mutuwa; ba’a san kuma inda shugaban ƙasa yake ba,” in ji Atiku.
Ya miƙa sakon ta’aziyyar sa ga jama’a da Gwamnatin jihar Benue, yana cewa “Muna tare da ku cikin jimami da goyon baya.”