Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Ɗan takarar shugabancin Najeriya na jam’iyyar PDP a zaɓen 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya gargadi shugaba Tinubu kan ce yawaitar ciyo bashin da ya ke yi.
Atiku ya ce yawan ciyo bashin zai ƙara jefa tattalin arzikin Najeriya cikin mawuyacin hali.
BBC ta rawaito, Atiku ya kuma soki yadda majalisar dokoki ke amincewa da buƙatar ciyo basussukan, waɗanda a cewarsa suke ƙara jefa ƙasar cikin ƙangin bashi.
“Rahoton da bankin duniya ya fitar kwanan nan, wanda ke nuna cewa Najeriya ce ƙasa ta uku da ta fi cin bashi daga hukumomin kuɗi na duniya abin damuwa ne”, in shi.
Majalisa ta nemi rundunar sojin Najeriya ta kawo ƙarshen Lakurawa.
Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Da Kwalejojin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki
Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya.
Ya ƙara da cewa Najeriya na ƙara nutsewa a cikin bashi, “sannan majalisar dokoki suna taimakawa.
Tinubu ya bayyana a watan Yuli cewa hukumar tattara haraji da kwastam sun tara kuɗin shiga da ba a taɓa tarawa ba. To me ya sa ake cin bashin? akwai wani abu da suke ɓoyewa ƴan Najeriya.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.