Deprecated: Unparenthesized `a ? b : c ? d : e` is deprecated. Use either `(a ? b : c) ? d : e` or `a ? b : (c ? d : e)` in /home/martabaf/public_html/wp-content/plugins/wp-socializer/core/templates/floating-sharebar.php on line 180
Atiku Ya Sake Kira Ga Gwamnatin Najeriya Ta Kafa Dokar Ta Baci. - Martaba FM
October 20, 2021

Atiku Ya Sake Kira Ga Gwamnatin Najeriya Ta Kafa Dokar Ta Baci.

Page Visited: 291
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:45 Second

Daga: Suleman Ibrahim Moddibo

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya bukaci ‘yan kasar su dai na biyan  ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane  kudin fansa idan har sun kwashi ‘yan uwansu, inda ya ce matakin na biyan diyya ga yan bindiga  zai haifar da illa nan gaba.

RFI Hausa ta rawaito cewar Yayin da ya ke tsokaci kan sace wasu karin dalibai da malaman su da ‘yan bindiga suka yi a Kaduna, Atiku ya sake kira ga gwamnatin Najeriya da ta kafa dokar ta baci kan harkar ilimi wanda zai bada damar samar da tsaro na sa’oi 24 akan kowacce makarantar dake yankin da ake fama da wannan matsala da jihohin dake makotaka da su.

Atiku ya ce ya zama wajibi a matsayin mu na kasa mu dauki kwararan matakai domin kawo karshen wannan sankarar satar dalibai a makarantu da kuma samar da manufofin da zasu kare daliban.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us