Wasu mazauna garin Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sun karyata rade-radin da ake ta yadawa na kwace wasu motoci biyu dauke da makamai daga hannun sojoji da wani dan bindiga mai suna Bello Turji ya yi.
Da ya ke zantawa da Daily Trust, wani mazaunin garin Zurmi ya ce ‘yan bindigar ba su taba kwace motocin daga hannun sojoji ba, sai dai sun same su makale a cikin daji suka banka musu wuta.
Ya bayyana cewa, wannan abin takaicin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kauyen Kwasabawa yayin da sojoji ke shiga daji domin gudanar da aiki, kwatsam sai ga motar su ta makale rabin hanya cikin daji.
“Bayanan da muka samu sun nuna cewa sojoji sun samu labarin cewa ‘yan bindigar na yin taro a wani wuri a cikin dajin, don haka suka yanke shawarar isa wurin da nufin yakar su amma basu kai ga karasawa ba motar ta tsaya.
Da farko sojoji da jami’an hukumar kare hakkin al’umma ta Zamfara (CPG) sun yi wa motocin sojojin gadin don hana ‘yan bindigan shiga su, amma daga baya suka yi watsi da su suka bar wurin.”
Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce da a ce sojoji sun samu karfin gwiwa a kan lokaci da lamarin ba zai faru ba; yana mai cewa ‘yan bindigar ba za su shiga motocin ba.
Ya ce: “A gaskiya ‘yan bindigar ba su yi wa sojoji harbin bindiga ba, sun kuma kwace motocin sojojin amma sai da sojoji suka bar wajen.
“A gaskiya sojoji sun zauna a kusa da motarsu na kusan rabin sa’a kafin daga bisani su bar wajen. Sojojin sun yi iya kokarinsu wajen ganin sun kare motocin amma ana zargin cewa an umarce su da su bar wurin.”
Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.
Ambaliya: Mutum Kusan 50 Sun Rasu In Da Dubbai Suka Rasa Muhallansu A Najeriya.
Crypto: Kotu ta Aike Wa Gwamnan CBN Sammmaci Don Ya Gurfana A Gaban Ta.
Shugaban ‘yan fashin, Bello Turji, da ‘yaransa, wadanda adadinsu ya kai 30, sun fito ne a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta na yanar gizo, inda ya ce sun kwace motoci daga hannun sojoji.
An ga ‘yan bindigar a cikin faifan bidiyon suna kwashe akwatuna biyu da ake zargin akwai harsasai da wasu kayayyaki daga cikin motar da aka bari.
Daily Nigerian
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
-
Akwai Bindigogin AK47 Guda Dubu 60 A Sansanonin Ƴan Bindiga Ɗari 120 Cikin Jihohin Arewa Masu Yamma,-Rahoto.
-
Wani Babban Kwamandan Sojin Isra’ila Ya Baƙunci Lahira A Gaza.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
-
Mutum Sama Da 20 Sun Mutu A Wani Harin Da Sojoji Su Ka Kai Kasuwa A Sudan.