Ba Mu Bayar Da Umarnin Al'umma Su Ɗauki Makamai Don Kare Kansu Daga Ƴan Bindiga Ba- Gwamnatin Katsina.
Daga Abdulrahman Salihu
Gwamnatin jihar katsina, ƙarƙashin jagoranci Malam Dikko Umar Radda, ta yi ƙarin haske kan bayanan da ke yawo bisa matakan da take dauka kan sha’anin tsaro.
A ranar Alhamis ne wasu rahotanni suka fara yawo a kafafen sada zumunta, in da ake yaɗa cewa, gwamnatin jihar ta yi umarni al’ummar jihar su ɗauki makamai domin kare kansu daga yan bindigar da suka addabi jihar tsawon lokaci.
To sai dai cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammad, ya fitar ta ce, kwamishinan tsaro da al’amuran cikin gida, Dr. Nasiru Mu’azu, ya ce gwamnatin jihar ba ta ba da umarni jama’a su ɗauki makamai don kare kansu daga harin ƴan ta’adda ba.
“Gwamnatin jiha ɗauki matakan karta kwana ne wajen shawo kan taɓarɓarewar tsaron da ya addabi ƙauyuka musamman ƙananan hukumomi shida da ke faɗin jihar”, in ji Dakta Mu’azu.
Ya kuma ce gwamnatin jihar ta ƙaddamar da tsarin ba da horo ga ƙungiyoyin sa kai tare da samar musu da bindigun buga ka laɓe tare da sauran kayayyakin da suka dace, domin ba da kariya ga al’ummar ƙauyukansu maimakon ba da dama ga daidaikun jama’a mallakar makaman.
A ƙarshe ya ce gwamnatin jihar Katsina za ta cigaba da tabbatar da tsaron al’ummar jihar tare da cigaba da haɗin gwiwa da hukumomin tsaro a matakin tarayya domin tabbatar da zaman lafiya a fadin jihar.
Ƴan bindiga a jihar Katsina da wasu jihohin Arewacin Najeriya, sun jima suna cin karen su ba babbaka, in da suke garkuwa da kuma kashe ko raunata mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba, tare da raba da dama da muhallan su, in da hukumomi ke cewa suna yin nasarar kakkaɓe ayyukan ƴan bindigar.