December 21, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Babban Sifeton Ƴansanda Ya Umarci Jami’ansa Su Janye Daga Sakatariyar Ƙananan Hukumomin Jihar Rivers.

Wasu rahotanni daga jihar Rivers na cewa, babban Sufeto na ƴansandan Najeriya ya ba da umarnin janye jami’ansu da su ka mamaye sakatariyar ƙananan hukumomi a Rivers na tsawon watanni uku.

An mamaye sakatariyar ne a watan Yuni sakamakon rashin jituwar da aka samu tsakanin shugabannin kwamitin riko da ke goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara da kuma shugabannin kananan hukumomi da suka sauka, wadanda suka kasance masu biyayya ga Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT).

Fadar Shugaban Najeriya Ta Karrama Shugaban Makarantar Sakandare A Jihar Zamfara.

Kuskuren Jaridar Daily Trust Da Yadda Gaskiya Ta Bayyana Game Da Yarjejeniyar Samoa.

Gwamnan Jihar Zamfara Ya Biya Naira Biliyan 9 Ga Ƴan Fansho.

Daily Trust ta rawaito cewa sai dai a yau Litinin, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴansanda a jihar Rivers, SP Grace Iringe-Koko, ya ce sabon kwamishinan yansandan jihar, CP Bala Mustapha, ya mika umarnin babban sufeton ‘yan sanda, IGP Kayode Egbetokun. domin a janye dukkan jami’an da aka tura a baya don rufe sakatariyar da kuma tsare ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *