Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Babban Bankin Najeriya CBN, yace za a cigaba da amfani da kudaden naira kamar yadda yake bisa tsarin doka.
Express Radio ta rawaito cikin wata sanarwa da CBN ya fitar ta ce, ya lura akwai ƙarancin gilmawar takardar Naira a wasu daga cikin biranen kasar, wanda hakan yakan faru a harkokin cinikayya na yau da kullum.
CBN ya ƙara da cewa za a cigaba da karbar takardar naira bisa tsarin doka ta 2007, sashin na 20(5) inda ya ce yace babu wanda zai daina karbar kudaden Naira da CBN ya samar.
Sanarwar ta shawarci Jama’a da su ci gaba da amfani da takardun ntaira batare da jin wani ɗar ba.
A baya ne dai babbar kotun ƙolin ƙasar ta yanke hukunci kan cewa za a dena karɓar tsofaffi kuɗaɗen ƙasar a ƙarshen watan Disamba na shekarar 2023, bayan wata ƙara da wasu gwamnonin ƙasar suka shigar, inda suka nemi kotu ta hana CBN chanza kuɗin ƙasar da ya yi a lokacin, wanda hakan ya sa ƴan Najeriya cikin tasku.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.