Shugaban Majalisar Dokokin jihar Delta Hon. Dennis Guwor, ya bayyana cewa babu wani gurbi a gidan gwamnati jihar Delta, yana mai cewa jama’ar jihar za su sake kaɗa kuri’a ga Gwamna Sheriff Oborevwori a zaɓen shekarar 2027, domin ya ci gaba da wa’adin sa na biyu.
Guwor wanda ya bayyana hakan lokacin da ya karɓi baƙuncin shugabanni da mambobin ƙungiyar “Unique Ladies for Sheriff” a gidan sa da ke Asaba, ya kuma bayyana cewa Oborevwori shi kaɗai ne zai kasance ɗan takarar gwamna a jihar Delta a shekarar 2027.
Tare da matar sa Timiebi a gefensa, Guwor ya tabbatar da cewa gwamnan zai ci gaba da cika alkawurran da ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaben sa, kuma ba zai bari wani ya karkatar da hankalin sa ba, duk da yadda wasu ke kokarin kawo masa cikas.
Ya kara da cewa “A shekarar 2027 za a samu dan takarar gwamna guda ɗaya tilo a jihar Delta. Gwamnan mu, Mai Girma Hon. Sheriff Oborevwori, mai gudanar da aiki ne, wanda aikinsa ke magana da kansa. Ya yi ƙoƙari matuƙa, kuma mutanen Delta na alfahari da shi.
“A 2023, jam’iyyar mu ta samu nasara a ƙananan hukumomi 21 daga cikin 25. Amma a 2027 za mu lashe duka 25 daga cikin 25. Ba za a sake barin wata ƙaramar hukuma ta shiga hannun wata jam’iyyar hamayya ba. Mambobin Majalisar Dokokin jihar Delta za su tsaya tsayin daka tare da Gwamna domin ya ci gaba da inganta ci gaban jihar cikin hanzari.” Inji shi.
Shugaban Majalisar ya yaba wa ƙungiyar matan bisa goyon bayan da suke bai wa Oborevwori, da kuma yadda suke haɗa kai don samun nasarar sake zaben sa.
Tun da farko shugabar ƙungiyar ta kasa Unique Dame Nkem Okwuofu, ta bayyana cewa kungiyar ta kunshi mata ‘yan siyasa masu ƙarfi daga jam’iyyar PDP, da nufin tallafa wa Gwamna domin cigaban jihar ta fuskoki daban-daban.
Daga cikin waɗanda suka tarbi ƙungiyar akwai Mataimakin Shugaban Majalisar Rt. Hon. Arthur Akpowowo, da Shugaban Masu Rinjaye Dr. Emeka Nwaobi, da Mataimakin Shugaban mai tsawatarwa Fred Martins, da sauran su da dama.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP