January 22, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

“Bai kamata tsare- tsaren kuɗi da gwamnati ke son ingantawa ya fifita wasu jihohi ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba”- Atiku Abubakar.

Daga Fatima Suleiman Shu’aibu

Jagoran adawar Najeriya, Atiku Abubakar ya yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta yi aiki bisa gaskiya da riƙon amana wajen shirya taron jin ra’ayin jama’a kan sabon ƙudirin harajin ƙasar da ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar.

A makon da ya gabata ne majalisar dattawan ƙasar ta yi wa ƙudirin karatu na biyu, inda kuma yanzu ta miƙa shi ga kwamitin kuɗi na majalisar domin shirya
taron jin ra’ayin jama’a kan ƙudurin.

BBC ta rawaito, cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Lahadi, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, ya ce kan ‘yan ƙasa ya haɗu wajen yin kira a samar da tsare-tsaren kuɗi bisa adalci da daidaito ga kowane yanki.

Gwamnan Kano ya gana da ƴan majalisar wakilai na Kano Kano sabuwar dokar haraji.

NAHCON ta ce kowanne alhajin 2023 za a mayar masa da naira 60,080.

Gwamnatin Najeriya za ta raba irin Alkama mai jure zafi ga manoma.

“Mun faɗa da babbar murya cewa bai kamata tsare- tsaren kuɗi da gwamnatin ƙasar ke son ingantawa ya fifita wasu jihohin ƙalilan ta hanyar ruguza sauran ba”. in ji Atiku Abubakar.

“A matsayina na mai ruwa da tsaki, na yi imanin cewa gaskiya da adalci da riƙon amana da kyakkyawan shugabanci, na da matuƙar muhimmanci wajen tsara manufofi”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *