December 2, 2021

Ban Sani Ba Ko An Bada Kudin Fansa Wajen Sako Mahaifinmu – Dan Sarkin Bungudu.

Page Visited: 99
0 0
Read Time:52 Second

A daren Asabar 16 ga watan Oktoba `yan binga suka Sako sarkin bungudu Alhaji Hassan Attahiru bayan ya shafe kwanaki 32 a hannun su.

Abdurrahman Hassan Attahiru, wanda shine babban dan sarkin ya tabbatar wa da BBC sako sarkin maifin nasu

Ya ce, an sako mahaifin na su a cikin koshin lafiya sai dai dan abin da ba a rasa ba saboda tsawon lokacin da ya kwashe a wajen ‘yan bindigar.

Dan sarkin ya ce, kannan mahaifinsa da jami’an ‘yan sanda da mambobin kungiyar Miyetti Allah da kuma gwamnatin jihar Zamfara ne suka karbo mahaifin na sa daga hannun wadanda suka sace shi.

Abdurrahman Hassan Attahiru, ya ce, mahaifin nasu bai musu wani Karin bayani ba tun bayan dawowar sa gida game da yanayin da ya kasance a hannun ‘yan bindigar.

Sai dai ya ce, batun ko an bada kudin fansa wajen sako mahaifinmu ni ban sani ba saboda ban san komai ba a kai don kannan mahaifinmu ne a kan komai tun bayan da aka sace shi, in ji dan sarkin.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *