Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta ɗauko hanyar magance matsalar cin hanci da rashawa ba, wanda hakan ke zama babbar barazana ga ci gaban tattalin arzikin ta.
RFi ta rawaito, Bankin da sauran masu ruwa da tsaki sun buƙaci gwamnati da ta yaƙi ayyukan cin hanci da rashawar domin ita kaɗai ce hanya ɗaya tilo ta bunƙasar tattalin arziƙi.
Tinubu na son ganin babu wanda ya kwana da yunwa a Najeriya – Minista.
Dillalan fetur sun nuna damuwa kan tsaikon da ake samu a matatar Fatakwal.
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
A wani taron tattaunawa kan halin da aikin yaƙar cin hanci da rashawa ke ciki a Najeriya wanda ƙungiyar Agora Policy haɗin gwiwa da gidauniyar MacArthur suka shirya a jiya Talata, mahalarta taron sun nemi a sauya fasalin tsarin siyasar Najeriya da na shari’a tare da gina manyan hukumomin yaƙi da rashawa.
Wakilin Bankin Duniya a Najeriya, Ndiame Diop ya ce cin hanci ya zama babban ƙalubale ga fannin tattalin arziƙin ƙasar, inda ya ƙara da cewa samar da tsaftataccen tsari a aikin gwamnatin ƙasar ya zama babban al’amari da aka kasa cimmawa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rasuwar Sheikh Idris: mun “fawwala komai ga Allah maɗaukakin Sarki”- Gwamnan jihar Bauchi.
-
Kotun koli ta soke hukuncin da ya bai wa tsagin da ke adawa da Obi a jam’iyyar LP nasara
-
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027
-
Hakeem Baba ya sauka daga muƙamin mai bai wa Tinubu shawara ta musamman kan al’amuran siyasa.
-
Hukuncin kotun sauraron ƙorafi kan zaɓen jihar Edo “babban kuskure ne da tauye adalci”-PDP