Daga Sadiq Muhammad
Babban Bankin Duniya (World Bank) ya yaba da yadda gwamnatin Jihar Jigawa ke gudanar da aikin Agro-Climatic Resilience in Semi-Arid Landscapes (AcReSAL) cikin gaskiya, jajircewa da kuma hadin kai.
Wannan yabo ya fito ne daga Dr. Joy Agene, shugabar tawagar AcReSAL, yayin ziyarar ban girma da ta kai wa Gwamna Malam Umar Namadi a gidan gwamnati da ke Dutse.
Cikin ta sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel, Dr. Joy Agene ta ce “Gwamna, kai ne ɗaya daga cikin shugabanni mafi gaskiya da rikon amana da muka taɓa aiki da su. Jama’ar jihar Jigawa sun yi sa’a da kai.”
Ta jaddada cewa a cikin tantancewar da aka yi kan ayyukan da Bankin Duniya ke daukar nauyi, jihar Jigawa ta fito fili a matsayin ɗaya daga cikin jihohin da suka fi nasara a ƙarƙashin shirin AcReSAL.
“Jigawa ta na taka rawar gani a duk tarurrukan da muke yi da sauran jihohi. Tsarin aiki da haɗin kai tsakanin ma’aikatunta abin koyi ne.”
Dr. Agene ta bayyana cewa ziyarar da suke yi na da nufin duba ayyukan da ake yi, gano wuraren da ake bukatar gyara, da bayar da shawarwari domin inganta aiwatarwa.
A nasa jawabin, Gwamna Namadi ya godewa Bankin Duniya da tawagar Dr. Agene bisa wannan yabo da goyon baya da suke baiwa Jigawa.
“Ayyukan AcReSAL sun kawo canji mai kyau ga rayuwar jama’ar Jigawa. Sun taimaka a fannonin ruwa, gyaran kwaruruka, da hana kwararar hamada.”
Ya bayyana Dr. Agene a matsayin abokiyar ci gaba mai gaskiya, kuma mai kishin aiki, tare da tabbatar mata da cewa Jigawa za ta ci gaba da tabbatar da dmɗorewar shirin.
Shirin AcReSAL ya na da nufin magance ƙalubalen yanayi da muhalli a yankunan da ke fama da fari ta hanyar kula da ƙasa da ruwa da kuma ƙarfafa rayuwar al’umma.