Daga Fa’izu Muhammad Magaji
Wata kotun shari’ar musulimci mai lamba 2 da ke Tashar Babiye a karamar hukumar Bauchi , ta aike da amarya da ango zuwa gidan gyaran hali, su ci amarcinsu a can, kafin ranar da za a yanke musu hukunci, bayan kotun ta samunsu da laifin hadin baki, da muzguna wa dan kishiyarta, tare da jimasa munanan raunuka.
Tin da farko ‘dan sanda mai gabatar da ‘kara Luka Godiya, yace a ranar 19 ga watan Agusta na wannan shekarar ta 2022, da misalin karfe 12 na rana, wasu membobin ‘yan kwamitin unguwar Bauchi, da ke cikin garin Bauchi, suka garzaya ofishin yan sanda suka kai karar wani mai suna Yusuf sani, da amaryarsa Na’ima Ahmed, wanda aka samesu da hada baki, da muzguna wa dansa, da yi masa azaba, kana da masa horo da kin bashi abinci, da mummunar duka ga yaron mai suna Walid Yusuf dan shekara 6, wanda saboda dukan Walid ɗin yasa ya samu munanan raunuka a jikinsa, da idonsa.
Dan sandan ya kara da cewa a lokacin da yaga Walid ɗin bai taba tunanin zai rayuba, sakamakon irin halin da ya ganshi ciki.
Luka Godiya, ya kuma ce, ana dukan yaron ne, saboda da babu mahaifiyarsa a gidan, kana mahaifin yaron ma yana dukan yaron, da kuma kishiyar mamansa, wato amaryan babansa kenan.
Amaryar takan daure yaron a gida, wani lokaci ma takan aiki yaron gurin da bai dace ace dan shekara 6 yana zuwa gurin, ko ana aikansa da daddare ba.
Aikata hakan laifine da yasaba wa kundin laifuffuka sashi na 125,213, 217, na tsarin dokar Penel Code.
Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kano Za Ta Maka Hukumar Aikin Hajjin Najeriya A Kotu.
Kotu Ta Yi Fatali Da Buƙatar Abdujabbar Kan Neman Sauya Masa Kutu.
Kotu Ta Aike Da Ɓarawon Da Ya Yiwa Ɓarawo Sata Gidan Gyaran Hali.
Bayan karantawa amarya da ango kunshin tuhumen tuhumen da ake musu, sun amsa laifinsu.
Inda Mai shari’a Barrister Muktar Adamu Bello Dambam, ya aike da mahaifin yaron tare kishiyar mahaifiyarsa, zuwa gidan gyaran Hali, ya kuma daga sauraron shari’ar zuwa ranar 29 ga watan Agusta na shekarar 2022.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Shanun Sun Yi Zanga-zangar Ce Don Rashin Cika Alƙawuran Gwamnati A Indiya.
-
Ana Ƙoƙarin Ceto Rayukan Kifaye Sama 100 A Australia.
-
Budurwar Ta Kai Kanta Ga Ƴan Sanda Ne Bayan Saurayin Ta Ɗan Ƙasar Turkiyya Na Neman Ta Ruwa A Jallo.
-
Ango Da Amaryar Da Aƙali Ya Aike Su Gidan Ɗan Kande Bayan Zargin Azabtar Da Ɗan Kishiyarta.
-
Kwamandan ’yan fashin daji zai auri daya daga cikin fasinjan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.