Bauchi: Jam`iyyar APC Akwai Babbar Nasara Abubakar Sadik Ya Rungumi Mutane,- Bashir Mali.

Page Visited: 1250
0 1
Read Time:1 Minute, 29 Second

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

An kira ga al`ummar jihar Bauchi baki daya su bawa ‘dan takarar gwamnan jihar Bauchi a jam`iyyar APC Air Mashal Abubkar Sadik ‘kuri`unsu domin ya zama gwamnan jihar Bauchi a babban za’ben shekarar 2023.

Wani matashin ‘dan siyasa a jihar Bauchi Alhaji Bashir Umar Mali, ne ya yi wannan kiran ta cikin wani shirin kai tsaye da aka yi dashi a Martaba FM.

A cewar Mali idan har aka za’bi Sadik to al`ummar jihar Bauchi za su mori gwamnati musamman ma matasan jihar da suke birni da karkara “hakikanin gaskiya jam`iyyar APC akwai babbar nasara kamar shi Air Mashal Baba Abubakar Sadik, ya rungimi jama`a”.

“Mun zauna da shi mun san wanene shi mun san ina aka dosa a cikin tafiyar kuma mun san makomar matasan jihar Bauchi, matukar aka yi Baba Abubakar Sadik,” in ji Bashir Mali.

NNPP: Halluru Dauda Jika Ne Zai Ci Zaɓen Gwamnan Jihar Bauchi A Zaɓen 2023- Kwamared Haruna.

Bauchi: Ɗan Takarar Gwamnan APC Abubakar Saddique Zai Iya Rasa Takarar Sa.

Nan Gaba Kaɗan Ake Sa Ran Shekarau Zai Fice Daga Jam’iyyar NNPP Zuwa PDP.

Ya kuma kara da cewar Baba Sadik, ‘dan takarane da yazo da shirin cin za’be da kuma saukin talla “ba a ta’ba samun ‘dan takarar gwamnan da ya zo jihar Bauchi ba, ya ke da abin fa’da irin Baba Abubakar ba, ayyukansa a zane suke kuma a kasa suke, wanda kowa ya gani kuma mutane suna mora, kuma ba wai jihar Bauchi bace ka’dai Najeriya ya yiwa aiki, ya yi abubuwa da yawa wanda mu ba zamu manta da shi ba, irin su Baba Sadik. mutane ne wanda ake bukatar su a jihar Bauchi dama Arewacin Najeirya da kasar baki daya.”

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Siyasa

2023: Ƴan Takarar Shugabancin Najeriya Sun Sanya Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya.

Ƴan Takaran zaben shugaban kasar Najeriya da za’ayi a shekara mai zuwa, yau sun rattaba hannu akan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe da kuma tabbatar da gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Yayin wani biki da akayi a birnin Abuja da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ya jagoranta, ‘yan takarar zaben da suka […]

Read More
Siyasa

Ƴan Sanda Sun Gargaɗi Masu Ɗauƙar Makamai Da Kayan Maye A Lokacin Yaƙin Neman Zaɓe.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo Rundunar yan sandan jihar Kano a Arewa maso Yammacin Najeriya, ta ja hankalin yan siyasa bisa yaƙin neman zaɓe mai tsafta. Jan hankalin rundunar ya zo ne a dai dai lokacin da hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya INEC, ta buɗe damar yaƙin neman zaɓe a hukumance. Kwamishinan ƴan sandan […]

Read More
Siyasa

Kishin Ƙasa Shi Ne Tubalin Jagorancin Al’umma, Raunin Jagoranci Shi Ke Haifar Da Rashin Adalci,-Obasanjo.

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce kasar na bukatar gwamnatin da ta san yadda ake gudanar da mulki. Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito tsohon shugaban na wannan maganar a wurin taron bikin cikar makarantar Kings college ta Legas – daya daga cikin tsoffin makarantu a kasar – shekara 113 da kafuwa. Mista […]

Read More