December 21, 2024

Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

An tabbatar da mutuwar mutane 20 galibi mata da yara ƙanana sakamakon wani hatsarin jirgin ruwa a kogin Benue a ranar Asabar a kusa da Ocholonya a ƙaramar hukumar Agatu.

Daily Trust ta rawaito, jami’in hulɗa da jama’a na Ƴansandan jihar SP Catherine Anene, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Lahadin da ta gabata, ya ce an fito da gawarwakin mutane 20 tare da ceto mutane 11 da rai.

Anene ya ce, “An tabbatar da lamarin kuma ana ci gaba da aikin ceto.

Rahotanni sun ce waɗanda abin ya shafa sun koma Doma ne a jihar Nasarawa bayan sun halarci wata kasuwa a ƙauyen Ocholonya lokacin da kwale-kwalensu na katako ya kife.

Kawo Ƙarshen Yin Shiru: Juriya, Jajircewa Da Ci Gaba Wajen Magance Cin Zarafin Mata Da Yara a Jihar Yobe.

Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.

Sallamar da Gwamna Abba ya yi wa Sakataren Gwamnati da Kwamishinoninsa 5.

Wani mazaunin Ocholonya, mai suna Adanyi, ya faɗawa yan jarida a Makurdi, cewa, “A ranar Asabar ita ce ranar kasuwar Ocholonya, jirgin ruwan ya na ɗauke da mata da yara ne ya koma Odenyi a jihar Nasarawa lokacin da ya kife, kuma kowa ya nutse.”

Shima shugaban ƙaramar hukumar Agatu, Melvin James, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho da Daily Trust a ranar Lahadi, ya na mai cewa hakan ya faru ne da misalin karfe 7 na yammacin ranar Asabar.

Ya ce waɗanda abin ya shafa ‘yan kasuwa ne daga al’ummomin Apochi da Odenyi da ke Doma jihar Nasarawa.

“An sanar da ni game da lamarin, kuma rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 20 sun mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *