Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta kama babban sakataren ma’aikatar ƙananan hukumomi Ibrahim Muhammad Kabara, da kuma shugaban karamar hukumar Tarauni, Abdullahi Ibrahim Bashir, da kuma wasu mutane biyar, da ake zarginsu da hannu a badaƙalar kwangilar magungunan ƙananan hukumomi Kano 44.
Kazalika hukumar ta aike da takarda gaiyata ga shugaban rukunin shagunan magani na NOVEMED, wanda ɗa ne wurin tsohon Gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ne ya ba da umarnin a yi binciken gaggawa kan zargin badaƙalar wadda Ɗan Bello ya bangakaɗo a wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta.
APCin Kano Na Son EFCC Ta Yi Bincike Kan Bidiyon Ɗan Bello.
Za A Ɗauki Ma’aikata Sama Da Dubu 40 Domin Aikin Zaɓen Ƙananan Hukumomi A Kano.
NNPP Ta Umarci Masu Son Yi Takara A Jam’iyyar Su Ajiye Muƙamansu.
Premier Radio ta rawaito, hukumar na tuhumar mutane da saɓawa dokokin tsarin aikin gwamnati, ta hanyar aiwatar da kwangilar da bata cika ƙa’ida ba, ba tare kuma da sahalewar gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ba.
Wata majiya ta ce, tuni shugaban ƙaramar hukumar Tarauni, ya amsa laifin sa, In da ya tabbatar da cewa, ya bayar da da umarni ba bisa ƙa’ida ba, na biyan sama da naira millyan 402 cikin kudaden siyan magunguna ga ƙananan hukumomin jihar Kano.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.