Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Radda, ya ce ƴan bindiga ba za su iya gudanar da ayyukansu cikin walwala ba, fa ce tare da hadin gwiwar wasu ɓatara gari a cikin al’umma.
Malam Dikko Radda, ya bayyana hakan ne wani taro da ya yi Daura, in da ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tallafa wa jama’a domin taimaka wa jami’an tsaro wajen kare al’umma daga hare-haren ƴan fashin daji masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Domin cimma wannan muradun gwamna Dikko ya ce sun bullo da wani shirin ɗaukar matasa masu ƙokarin kare al’ummominsu domin basu horo da sauran kayan aiki da suke bukata domin tinkarar ƴan bindiga.
Gwamna Radda ya bayyana muhimmacin jajircewar al’umma domin ta kare kanta saboda, wasu kauyuka kafin jami’an tsaro su isa, bata gari za su iya cin karensu kuma su fice, inda ya bada misali da wata ziyara da ya kai wani kauye.
“Na je wani kauye mai suna Tsamiyar-jino, sai da na kwashe sa’o’i biyu kafin na isa duk da cewa da mota kirar jeep.Don haka, idan ƴan bindiga suka kai hari irin wadannan wuraren, daga lokacin da ka sanar da jami’an tsaro, za su ɗauki sama da sa’o’i biyu kafin su iya amsa kiran da ake yi musu, kafin zuwan jami’an tsaro za su iya yin duk abin da za su yi, Za su kashe mutane kuma sun yi garkuwa da wasu.
Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.
Ƙungiyar Limamai A Najeriya Na Son Gwamnati Ta Gyara Matatun Mai Na Ƙasar.
Gagarumar Zanga-zanga Ta `Barke A Isra’ila Yayin Hezbollah Ke Zafafa Hare-hare Kan `Kasar.
Dikko Radda ya jaddada cewa wannan yakin ba na jami’an tsaro ne su kadai ba, sai da taimakon al’umma, saboda ƙarancinsu.
“Na sha fada cewa jami’an tsaro ba za su iya yin wannan aikin su kadai ba. Ba ma da wadatar su. Ina mamakin yadda muke mutuwa ta wulakanci. An gaya mana cewa duk wanda ya mutu don kare iyalinsa zai shiga aljanna”.
“Za ka ga wasu miyagu guda biyar suna kai hari ga al’ummar 2,000 zuwa 3,000, suna yi wa ƴaƴa mata fyade, da kuma sace wasu ba tare da wata arangama da mutanen wannan unguwar ba. Idan akwai matasa 100 a cikin al’umma da suka tunkare su, ba za su yi harbi sama da sau uku ba tare da an kama su da hannu ba.
“Biyan kudin fansa ba ya ma hana ƴan bindiga kashe wanda aka yi garkuwa da shi, wani lokaci sukan ƙarbi ƙudin su kashe wanda suka kama.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.