Wani babban jigo a jam’iyyar NNPP, Buba Galadima, ya karyata jita-jitar cewa tsohon dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma jam’iyyar APC, ya na mai cewa babu wannan batu.
Hikima Radio ya rawaito a hirarsa jaridar The Guardian, Galadima ya ce babu wani mai cikakken hankali a Kano ko a wani bangare na Najeriya da zai yi alfahari da cewa ya na jam’iyyar APC ƙarƙashin Ganduje, ya zargi shugaban jam’iyyar ta APC da amfani da NNPP domin neman shahara a kafafen yaɗa labarai.
Da ya ke ba da amsa kan komawar Kwankwaso APC, Buba ya ce “Daga gare ku na fara jin wannan magana. To idan mun koma APC, Ganduje ne ma zai sanar da ’yan Najeriya? Ai saboda Ganduje ma kadai, babu wanda zai so komawa APC”.