August 8, 2022

CAN, Ta Bijirewa El-Rua’i Kan Rage Kwanakin Aiki.

Page Visited: 857
0 0
Read Time:56 Second

Kungiyar Kiristocin Najeriya reshen jihar Kaduna, CAN, ta yi watsi da matakin gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufa’i na rage kwanakin aiki ga ma’aikatan gwamnati daga biyar zuwa hudu.

BBC Hausa ta rawaito cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Rabaran Joeshep Hayaf ya aike wa manema labarai a ranar Talata, CAN ta ce kada ma’aikatan gwamnati su yadda da wannan batu, domin kada a yi musu sakiyar-da-ba-ruwa sai nan gaba a fito da wani abu da ba su san da shi ba.

”Ta yaya jihar da ke fama da matsalar tsaro, za a zo ace wai mutane su koma gona, alhalin gonakin a wajen gari suke, Mai zai faru idan su na gonar ‘yan bindigar suka far musu a gona, ko kuma aka shiga gidajensu?

Ma’aikata su tabbatar ba wani salo aka bullo da shi, sai nan gaba a shayar da su mamakin an rage musu albashi tun da ba aikin kwanaki biyar a mako kamar yadda aka bisa al’ada ake yi,” in ji Hayaf.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *