Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta fitar da wata takarda, da ke sanar da samar da sabbin takardun kudi na N5,000 da N10,000.
Takardar da ake cewa CBN ya fitar, wadda ta yadu sosai a kafar sadarwar WhatsApp da Facebook, an karyata ta ne ta hannun babban bankin a cikin wata sanarwa da aka fitar, ta shafin sa na X (wanda a da ake kira Twitter).
Takardar bugin da aka jingina wa CBN ta yi ikirarin cewa: “Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shigowar sabbin nau’ikkan takardun kudi guda biyu da suka hada da N5,000 da N10,000, a matsayin wani bangare na kokarin saukaka hada-hadar kudi da inganta sarrafa kudaden kasa.”
Sai dai babban bankin ya musanta wannan ikirari, yana mai bayyana shi a matsayin karya.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta ficewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta MNJTF.
-
Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta yi wa ƴan luwaɗi da maɗigo rajista a jihar.
-
Ɗan banga ya harbe kansa a ƙoƙarin bin wanda ake zargi da aikata laifi a Abuja.
-
Sarkin Musulmi ya shawarci gwamnonin Najeriya da su kawar da bambanci tsakanin ƴan asalin jiha da baƙi.
-
Sojojin Najeriya sun yi nasarar rage ayukkan ƴan ta’adda a jihohin Kebbi da Zamfara.