Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta aika sammaci ga Gwamnan Babban Bankin Ƙasa, Olayemi Cardoso da ya bayyana a gabanta game da shari’ar da ake yi wa kamfanin crypto na Binance.
The Cable ta rawaito cewa kotun ta ce Cardoso zai bayyana gaban ta da wasu takardun bayanai a ranar 2 ga watan Satumba.
Duk da cewa, mai shari’a Emeka Nwite ya dage zaman kotun zuwa 11 ga watan Oktoba, lauyan waɗanda ake ƙara ya buƙaci kotun ta sake sanya ranar zaman.
Kotu: An Tsare Ɗan Jarida A Gidan Yari Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamnan Kano Abba.
Gwamnatin Najeriya Ta Bai Wa Ƴan Kasuwa Wa’adin Tata Ɗaya Su Rage Farashi.
Amnesty Ta Nemi A Saki Ɗan PDPin Da Ke Tsare A Sokoto Kan Wallafa Bidiyon Gwamna Da Matarsa.
Daily Nigerian ta ce, a watan Afrilu ne dai, hukumar EFCC ta gurfanar da shugaban kamfanin Binance, Tigran Gambaryan kan zargin badaƙalar kuɗi.
Haka kuma, hukumar tattara haraji ta kasa tana tuhumar Binance da laifin kaucewa biyan haraji.
Kotun dai ta bukaci Gwamnan CBN ya bayyana gabanta ko ya tura wakilci.
Haka kuma, kotun ta mika sammaci ga shugaban sashin shari’a na CBN.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.