Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Gwamnatin jihar Yobe ta ƙaryata rahotanni da ake yaɗawa cewa, aƙalla sama da yara 200 cutar Sanƙarau ta kashe.
A wani taron manema labarai a birnin Damaturu, kwamishinan lafiya na jihar, Dakta Muhammad Lawan Gana, ya ce cutar sanƙarau ta kashe mutum 85 tsakanin Janairu da Afrilu sakamakon ɓarkewar cutar a jihar.
BBC Hausa ta rawaito cewa, kwamishinan ya ce, fiye da marasa lafiya 2,510 da suka kamu da cutar a jihar sun samu sauƙi kuma an sallame su daga asibiti.
Dakta Gana ya kuma ce an tura jami’an lafiya na sa kai sama da 200 zuwa sassan ƙananan hukumomin Poyiskum da Fika a wani ɓangare na ƙoƙarin da ma’aikatar take na daƙile cutar.
Ya ce ma’aikatan lafiya sun bi gida-gida domin ganowa tare da tura mutanen da ke da cutar asibiti.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.