Siyasa
Trending

Da Gaske Ne Shugaban APC Ganduje Zai Yi Takarar Shugaban Ƙasa A Zaɓen 2027?

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A ranar Lahadi ne wasu hotuna suka karaɗe shafukan sada zumunta, in da suke nuna tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban riƙo na jam’iyyar APC a Najeriya Abdullahi Umar Ganduje, na yin takarar shugaban ƙasar Najeriya in da gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma ke biye masa a matsayin mataimaki.

Shin da gaske ne batun takarar?

Yayin da hotunan suke ci gaba da yaɗuwa a ƙasar, shugaban jam’iyyar ta APC ya ce, ƙarya ce tsagwaronta wasu bata gari ke yaɗa wa.

Cikin wani wata sanarwar da mai magana da yawun Gandujen Edwin Olofu ya fitar, ya yi zargin wasu bata gari ne haɗin gwiwa ƙungiyar Kwankwasiyya ke yaɗa hotunan da nufin ɓata tsakanin Ganduje da shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu.

“Ganduje ya na ci gaba da kasancewa mai biyayya da kuma goyon bayan ayyuka da shugabancin Tinubu, wanda yake fatan samar da ci gaba da haɗin kai a ƙasa'”, in ji shi.

Ana dai ta samun tankiya tsakanin Ganduje da ƴan Kwankwasiyya a jam’iyyar NNPP wadda tsohon gwamnan Kano Rabi’u Musa Kwankwaso ke jagoranta, in da ake samun musayar kalamai masu zafi da suke ta da hazo a siyasar Kano da Najeriya.

Ko a cikin Makon nan sai da shugaban APC Ganduje ya nemi gwamnatin Najeriya ta bincike gwamnatin jihar Kano, kan zargin shirya zanga-zanga da ta kawo tarzoma, ko da yake ita ma gwamnatin Kanon ta zargi Gandujen da hayar ƴan dabar da suka tayar da hankali a yayin zanga-zangar lumana wadda ta rikiɗe zuwa rikici a jihar zargin da dukkanin su ke musantawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button