Labarai
Daga Ƙarshe Ɗan Ɗaban Da Ya Addabi Kano Abba Burakita Ya Mutu.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A makon da ya gabata ne wasu al’umma a birnin Kano suka yi kukan kura suka cafke Ɗan Daban a lokacin da ya fito kwacen waya da shi da yaransa, in da suka yi ta bugunsa har ta kai ga sun karairaya shi a hannu da ƙafa.
Kakakin Ƴansandan jihar Kano Abdullahi Haruna, ne ya tabbatar da mutuwar Abba Burakita a ranar Litini.
Kotu: An Tsare Ɗan Jarida A Gidan Yari Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamnan Kano Abba.
Iyalan Sarkin Kano Ado Sun Ƙaryata Alaƙa Da Zainab Wadda Take Iƙrarin Ita Ɗiyar Sarkin ce.
Kiyawa ya tabbatar da hakan ne a shafin sa na Facebook, in da ya ce ‘Ɗan Daban da muka kama, kuma dama muna nemansa abisa zargin laifukan fashi da makami da jagorantar harkar daba Abba Burakita, ya rasu,” in ji shi.