Daga Yanzu Duk Wani Ɗan Zamfara Zai Iya Mallakar Bindiga Domin Ya Kare Kansa.

Page Visited: 2546
0 1
Read Time:1 Minute, 15 Second

Gwamnatin Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta bai wa dukkan ‘yan Jihar damar mallakar bindiga domin kare kansu daga ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.

A wata sanarwa da Kwamishinan watsa labaran Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya aike wa manema labarai ranar Asabar, ya ce gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.

Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin ne watanni da dama bayan gwamnatin Jihar Katsina da ke makwabtaka ta umarci mazauna jhar su mallaki bindiga domin kare kansu daga masu kai hare-hare.

“Hare-haren ta’addanci sun kasance abin damuwa ga jama’a da gwamnatin jiha. Don haka ne, domin mu magance wannan matsala baki daya a yankunanmu, gwamnati ba ta da zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar shiryawa da kuma mallakar bindigogi domin kare kansu daga ‘yan fashin daji,” in ji sanarwar.

Ta kara da cewa gwamnati ta umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya bai wa dukkan mutanen da suka dace da kuma suke bukatar mallakar bindiga su mallake ta domin kare kansu.

Gwamnatin ta Jihar Zamfara ta ce ita da kanta za ta shige gaba wajen ganin an saukaka wa mutane hanyar mallakar bindiga, musamman ga “manoma domin samun makaman da za su kare kansu.”

“Tuni gwamnati ta kammala shirin raba fom 500 ga masarautu 19 da ke Jihar nan domin bai wa mutanen da ke bukatar mallakar bindigogi domin su kare kansu,” a cewar sanarwar.

Mun yanko wannan ne daga BBC Hausa

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tsaro

Masu Garkuwa Sun Bukaci A Basu Kudin Fansa Har Naira Miliyan 250 A Katsina Bayan Sun Sace Mutum 43.

Daga Suleman Ibrahim Maddibo wasu bayanai daga jihar Katsina da ke Arewa maso Yammacin Najeriya na cewa, al’ummar kauyen Bakiyawa da ke yankin Batagarawa na cikin firgici bayan da ‘yan ta’addan da suka sace mazauna kauyen 43 suka bukaci da a biya su naira miliyan 250 a matsayin kudin fansa, kafin sako mutanen da suke […]

Read More
Tsaro

Ƴan Sandan Bayelsa Sun Kama Wani Ƙasurgumin Mai Sace Mutane.

Rudunar yan sandan jihar Bayelsa ta ce ta kama wani da ake zargin rikakken mai satar mutane ne saboda fariyar da yake nunawa da dukiyarsa a shafukan sada zumunta. BBC Hausa ta rawaito, mutanesun san John Lyon ne, a matsayin ma’aikacin banki wanda a kullum rubuce-rubucen da yake wallafawa, na shawartar mutane su yi aiki […]

Read More
Tsaro

Sojoji Sun Halaka Ƴan Bindiga A Hanyar Kaduna.

Rundunar sojin Najeriya ta sanar da fatattakar ‘yan bindiga a yankin Fondisho da ke karamar hukumar Igabi kan hanyar Kaduna zuwa Zaria a arewacin kasar. BBC Hausa ta rawaito, tata sanarwa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya wallafa a shafinsa na Tuwita ranar Laraba ta ce sojojin sun samu kwararan […]

Read More