Wasu iyalai daga Kudancin California na jimamin rashi mai raɗaɗi na ɗansu mai kimanin shekaru goma sha uku Nnamdi Ohaeri Sr., wanda suka yi amannar ya mutu bayan ƙoƙarin yin wani kalubale da ke yawo a kafafen sada zumunta.
Nnamdi Sr. wanda aka fi sani da “Deuce,” shi ne babba a cikin ‘yan uwan sa huɗu, kuma yana da matuƙar sha’awar kiɗa da wasanni, musamman ƙwallon ƙafa. A matsayin sa na ɗan iyalan soja daga Murrieta, an san shi da saurin fahimta da barkwanci.
“Yabna da nishaɗi da hikima sosai,” mahaifin sa Nnamdi Ohaeri Sr., ya shaida wa tashar KTLA.
Iyalan sun tuna yadda suka kwashe lokaci ranar Lahadi biyu ga watan Fabrairu cikin farin ciki tare da shi.
“Mun dawo gida, mun yi wanka, muna kallon gasar Grammy. Yana matuƙar farin ciki da yadda Kendrick Lamar ke cin kyaututtuka,” in ji mahaifin sa.
Amma washegari da safe aka taras da Deuce a dakin sa ba ya motsi. Mahaifiyar sa ta gaggauta yin CPR yayin da mahaifin sa yai kiran lambar gaugawa 911 sannan ya gudu zuwa gidan maƙwabcin su neman taimako. Duk da ƙoƙarin su, likitoci sun tabbatar da mutuwar sa.
A farkon lamarin, iyayensa sun kasa fahimtar abin da ya faru, domin ba su yarda cewa ɗansu ya kashe kan sa ba. Sun bayyana shi a matsayin yaro mai nishaɗi da kyakkyawar fata ga rayuwa.
Binciken su ya kai su ga mamakin Deuce yayi ƙoƙarin gwada kalubale da ya gani a kafafen sada zumunta da ke buƙatar hana wa kai numfashi har sai mutum ya suma.
“Na ji wani labari game da wani yaro da ya gwada sa kansa domin ya suma, kuma daga baya ya farka,” in ji Ohaeri Sr.
Iyalan sun yi amanna cewa Deuce na iya jin labarin wannan kalubale daga abokan karatun sa, domin ba shi da shafin sada zumunta kuma wayar sa na ƙarƙashin kulawa ta iyaye.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
EFCC ta gurfanar da wasu mutum biyu kan zargin damfara da sunan A’A Rano
-
APC ta rufe hedkwatarta da ke Abuja.
-
An hallaka mutum 1 wani kuma ya jikkata kan zargin satar kare a jihar Bauchi.
-
Ɗiyata “ta yi aiki wa Buhari shekaru huɗu a ofishin Osinbajo ba tare da ko kwabo ba-Buba Galadima
-
Arewacin Najeriya ya fi Kudanci samun muƙaman Gwamnatin Tarayya- Fadar Shugaban Ƙasa