Daga Firdausi Ibrahim Bakondi
Wani direban mota da ya kashe masu shara guda Biyu a Legas a lokacin da yake yunƙurin kaucewa shiga hannun jami’an tsaro ya miƙa kansa ga ‘yan sanda.
Direban wata motar kirar Honda Saloon mai lamba EPE 984 DV da ake zargi da gujewa ƴan sanda ya murkushe wasu masu shara a babbar hanyar Legas, LAWMA, har lahira a unguwar Gbagada a ranar Litinin din da ta gabata.
Daily Trust ta rawaito, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da cewa direban motar ya miƙa kansa ga ‘yan sanda, kuma za a gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Laraba.
A halin da ake ciki, ma’aikatan tsaftar muhalli da ke aiki da a Hukumar Kula da Sharar tituna ta jihar Legas, LAWMA, a ranar Talata su ka yi watsi da kayayyakin aiki don alhinin rasuwar abokan aikinsu a hanyar Oshodi-Gbagada ta da ke Iyana-Oworo.
Mai magana da yawun hukumar ta LAWMA, Folashade Kadiri, wacce ba ta tabbatar da ko akwai wani umarni da aka ba ma’aikatan tsaftar muhalli da su kaurace wa yankin ba, ta kara da cewa al’ada ce masu shara a titi su rika jajanta wa abokan aikinsu a duk lokacin da wani abu ya faru dasu.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Sojojin Nijar sun kashe Mahara 29 a Tillaberi.
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.