September 22, 2021

Dokar Hana Makiyaya Yawo Da Dabbobin Su Baza Tayi Aiki Ba A Najeriya.

Page Visited: 88
0 0

Share with others !

0Shares
0
Read Time:1 Minute, 17 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Gwamnan Jihar Borno dake Najeriya Babagana Umara Zulum yace dokar hana Fulani makiyaya yawo da dabbobin su ba za tayi aiki ba a wasu jihohin kasar saboda halin da ake ciki.

Zulum yace abinda zai sa dokar tayi tasiri kamar yadda ake bukata shine magance matsalolin tsaron da ake fama da su yanzu haka da kuma matsalar tattalin arzikin da ta addabi jama’a.

RFI Hausa ta rawato Gwamnan yace ya zama wajibi a shawo kan matsalolin siyasa da tatatlin arzikin da suka shafi jama’a saboda illar da talauci tayi a Yankin Afirka ta Yamma abinda ke haifar da matsalar tsaro.

Zulum yace ana ci gaba da samun matsalar karancin abinci kuma yana da cikin matsalolin dake haifar rikice rikice, abinda ya sa gwamnatin jihar Borno ta kwashe shekaru 2 tana gabatar da bukatar ganin manoma sun koma gonakin su domin gudanar da harkokin su.

Gwamnan ya kuma ce bayan wadannan akwai batun sasanta manoma da makiyaya dake da matukar muhimmanci domin ganin sun fahimci juna da sanin irin gudumawar da kowanne bangare daga cikin su ke bayar wa domin samun zaman lafiya da rayuwa mai inganci.

Saboda haka Zulum yace wannan dokar da wasu gwamnoni ke barazanar fara aiki da ita ba za tayi tasiri ba, har sai sun zauna sun shawo kan wadannan matsaloli da ya ambata.

A ranar litinin Gwamnoni 17 dake kudancin Najeriya suka sanar da cewar daga ranar 1 ga watan Satumba mai zuwa zasu fara aiwatar da dokar hana yawon kiwo a jihohin su baki daya.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

0Shares
0
Get Social With Us