Sanata Ali Ndume, ɗaya daga cikin ƴan gaba-gaba wajen sukar ƙudirin ya ce a baya sun yi turjiya akan ƙudirin ne saboda neman a yiwa kowa adalci, domin haka abin da gwamnonin
suka yi, yunƙuri ne na samar da mafita.
A tattaunawarsa da BBC, Ndume ya ce akwai sauran abubuwan da ya kamata a gyara bayan matsayar da gwamnonin suka cimmawa.
“Abinda gwamnoni suka yi ci gaba ne, sai dai kwalliya ba ta gama biyan kudin sabulu ba, don har yanzu bamu san cikakken bayani akan dokokin ba,” cewar Ndume.
Sanatan ya ce ya kamata a ci gaba da jiyo shawarwarin sauran al’umma domin a tsaya kan mataki guda, “kuma a buɗe abun kada a yi hanzari, saboda shine zai kawo kuskure.”
“Yanzu dai an bude hanyar gyara, saɓanin da farko da aka rufe hanyar gyara ana cewa ayi yadda yake, yanzu sauran aikin yana hannun jama’a da ƴan majalisa”
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu dai ya gabatar wa Majalisar dokokin tarayyar ƙasar ƙudurin yin gyaran fuska ga dokar haraji ta ƙasar, lamarin da ya haifar da zazzafar muhawara da raba kawunan shugabanni a ƙasar.
Batun ya kai ga cewa shugaba Tinubu da Majalisar Dokokin Tarayya sun jingine batun muhawara da amincewa da dokar
har sai bayan an sake yin nazari a kanta.
A zaman da suka gudanar ranar Alhamis a Abuja, gwamnonin sun yi gyare-gyare ga ƙudurin harajin na shugaba Tinubu,
musamman ɓangaren rabon harajin cinikayya na VAT, wanda shi ne ya fi janyo cece-ku-ce.
Shawarar da gwamnonin suka cimma na nuna cewa sun rage yawan kuɗin harajin VAT da za a raba tsakanin jihohi bisa
la’akari da gudumawar da kowace jiha ta bayar wurin tara harajin.
Sai dai kuma shawarar gwamnonin ta ƙara yawan kason kuɗin a kan yadda yake tun asali.
Tun farko, sabon tsarin rabon harajin VAT da ke ƙunshe a ƙudurin yin gyara ga dokar haraji da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisar dokoki ya buƙaci a ware kashi 60 cikin ɗari ne domin rabawa gwargwadon gudumawar da kowace jiha ta bayar.
Wanda hakan ya nunka har sau biyu a kan asalin tsarin da ake amfani da shi na kashi 20 cikin ɗari.
Shawarar da gwamnonin suka yanke na nuna cewa an ƙara kashi 10 cikin ɗari a kan tsarin da ake amfani da shi a yanzu,
yayin da aka zabtare kashi 30 cikin ɗari daga abin sabon tsarin da shugaba Tinubu ya gabatar wa Majalisa.
BBC Hausa
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.