Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) reshen jahar Kaduna, ta cafke mutum 11 da ake zargi da aikata zamba ta intanet a karamar hukumar Chanchaga, Jihar Neja.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na X a ranar Lahadi, mai taken “EFCC Ta Kama Mutum 11 da Ake Zargi da Zamba ta Intanet a Neja,” ta bayyana cewa jami’an hukumar sun kwato motoci guda biyu da wayoyin salula 13 nau’uka daban-daban yayin kamen.
“Kamen da aka yi a safiyar Alhamis 27 ga watan Fabrairu 2025, a otal ɗin White, ya biyo bayan ingantaccen bayani na sirri da ke alaƙanta waɗannan mutane da ayyukan damfara ta intanet,” in ji sanarwar.
EFCC ta tabbatar wa jama’a cewa an gudanar da kamen cikin kwarewa, ba tare da wani cin zarafi ko sace wani ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa “Za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu da zarar an kammala bincike,”
Wannan kamen na zuwa ne mako guda bayan hukumar ta cafke mutum 59 a kan titin Abacha, da Mararaba, wata babbar hanyar da ta hada Abuja daga Jihar Nasarawa.
A lokacin wannan kamen, EFCC ta kwato wayoyin salula guda 73.
Hukumar ta bayyana cewa tana ci gaba da kokarin ta na yaki da laifukkan intanet da sauran nau’ukan zamba a faɗin ƙasar.