March 12, 2025

EFCC ta kama mutane fiye da 50 kan zamba ta Internet a Abuja.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta kama mutane hamsin da tara da ake zargi da aikata zamba ta intanet a Abuja.

EFCC ta bayyana hakan ne a shafin ta na X a ranar Laraba.

A cewar hukumar, jami’anta daga ofishin ta na Abuja ne suka gudanar da wannan kamen a ranar Litinin 24 ga watan Fabrairu, 2025.

Hukumar ta bayyana cewa “ta kama mutanen ne a kan Titin Abacha da ke yankin Mararaba Jihar Nasarawa, bayan samun sahihan bayanai kan rawar da suke takawa a ayyukan damfara ta yanar gizo,”

A yayin wannan samamen jami’an EFCC sun kwato wayoyin salula guda saba’in da uku na nau’uka daban-daban daga hannun waɗanda ake zargin.

Hukumar ta ce za ta gurfanar da su gaban kotu da zarar bincike ya kammala.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *