Daga Sani Ibrahim Maitaya
An karrama wani shugaban makarantar sakandare daga jahar Zamfara a matsayin wanda ya fi kowa kwazo a faɗin ƙasar nan da lambar yabo ta fadar shugaban ƙasa ta malamai daga makarantun najeriya a 2024.
Sakataren Gwamnatin Tarayya Sanata George Akume shine ya sanar tare da bayar da kyautukka ga malaman da suka lashe gasar ta shekarar 2024, a jiya a dandalin Eagle Square da ke Abuja a wani bangare na bukin ranar malammai ta bana.
A wajen taron, shugaban makarantar sakandaren Sambo dake Gusau, ya samu lambar yabo ta fadar shugaban ƙasa mafi girma a ɓangaren manyan makarantun sakandaren gwamnati dake ƙasar nan.
An baiwa shugaban makarantar Mallam Musa Yahaya Paila lambar yabo da kuma sabuwar Mota.
Gwamnan Jihar Zamfara Ya Biya Naira Biliyan 9 Ga Ƴan Fansho.
Kuskuren Jaridar Daily Trust Da Yadda Gaskiya Ta Bayyana Game Da Yarjejeniyar Samoa.
Ƴan Bindiga: Ƙofarmu A Buɗe Take Ga Duk Wanda Yake So Ya Miƙa Wuya- Tinubu.
Gwamnatin Najeriya ta yi bikin ranar malamai ta duniya ta 2024, wadda akeyiwa taken “Daraja da kimar malammai: Zuwa sabuwar yarjejeniya ta zamantakewar ilimi.”
Karin waɗanda suka yi nasara da suka fito daga makarantun gwamnati da masu zaman kansu na ƙasa, sun samu nasarar lashe motoci, da babura, da janaretoci, da sauran kayayyaki da dama.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Dokin rundunar Sojin Najeriya mai muƙamin Sajan ya mutu a Kaduna.
-
Ɓarawo ya mutu yayin da ya ke ƙoƙarin sata a cikin Taransifoma.
-
Yansadan jihar Adamawa sun fara bincike kan wasu mutum 2 da zargin sun yi wa yara mata biyu Fyade.
-
Yayin da Ƴansandan Kano su ka gargaɗi al’umma kan shiga cunkoso saboda barazanar tsaro gwamnatin jihar ta ce taron Mauludin Shehu Inyass ya na nan daram.
-
Wata gobarar tankar fetur ta ƙone direbanta a Ibadan.