Mutum hudu sun rasa rayukan su, yayin da wasu hudu suka jikkata bayan wani abu mai fashewa ya tashi, a ƙarƙashin wata motar haya a ƙaramar hukumar mulkin Biu ta jihar Borno.
Wannan fashewa ta faru ne a ranar Laraba 19 ga watan Maris, da misalin ƙarfe 2:30 na rana lokacin da wata mota kirar Golf 3 da Wakil Fari ke tukawa, ke kan hanyar ta daga Kimba zuwa garin Biu.
Bisa bayanan sirri da Zagazola Makama ta samu, wani ƙwararre kan yaƙi da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya ce bam din ya tashi ne a dai-dai lokacin da motar ta isa Sabon Gari a mahadar Kimba.
“Motar ta taka kan bam din ne lokacin da ta kai Sabon Garin, wanda hakan ya haddasa fashewa mai karfi,” kamar yadda rahoton ya bayyana.
Fashewar ta yi sanadin mutuwar fasinjoji hudu nan take, yayin da wasu hudu suka samu raunukka daban-daban. An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa Babbar Asibitin Biu domin samun kulawar likitoci.
Jami’an lafiya a asibitin sun tabbatar da mutuwar waɗanda suka rasa rayukan su, sannan suka mika gawawwakin su ga iyalan su bayan ajiye su a dakin ajiye gawa.
Hukumomi na zargin cewa ‘yan ta’adda masu alaƙa da ƙungiyar ISWAP ne suka dasa bama-baman, mai yiwuwa da nufin kai hari kan dakarun soja da ke aiki a yankin.
Bayan harin, jami’an tsaro sun kakkafa matakan tsaro a yankin tare da gudanar da bincike domin gano ko akwai wasu ƙarin bama-bamai da aka dasa, domin tabbatar da lafiyar masu amfani da hanya.
Haka kuma, hukumomin tsaro sun ƙaddamar da gangamin wayar da kai ga al’ummar yankin kan hatsarin da bam ɗin da bai tashi ba ke haifarwa, da kuma matakan kariya domin inganta tsaro.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta musanta ficewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta MNJTF.
-
CBN ya ƙaryata fitar da takardun kuɗi ƴan dubu 5 da dubu 10
-
Gwamnatin jihar Kebbi ta musanta yi wa ƴan luwaɗi da maɗigo rajista a jihar.
-
Ɗan banga ya harbe kansa a ƙoƙarin bin wanda ake zargi da aikata laifi a Abuja.
-
Sarkin Musulmi ya shawarci gwamnonin Najeriya da su kawar da bambanci tsakanin ƴan asalin jiha da baƙi.