Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wasa rahitanni daga `kasar Isra’ila na cewa, gagarumar zanga-zanga ta ɓarke a biranen Isra’ila, don neman gwamnatin ta dawo da ‘yan ƙasar da Hamas ke garkuwa da su a Gaza.
BBC ta rawaito masu shirya zanga-zangar sun ce kusan mutum 500,000 ne suka fantsama kan tittuna a Tel Aviv, tare da yi wa ginin ma’aikatar tsaron ƙasar ƙawanya.
Sannan ana gudanar da makamaciyar wannan zanga-zanga akai-akai a biranen Kudus da Haifa.
to sai dai yayin da zanga-zangar ke kara kankama, jami’an Isra’ila sun ce an kashe fararen hularta uku a wani hari da aka kai kan iyakar Jordan da Gaɓar Yamma.
Rahotonni sun ce maharin – wanda tuni sojojin Isra’ila suka kashe – direban motar dakon kaya ne, wanda ya taso daga Jordan, sannan ya tsaya a shingen binciken ababen hawa ya kuma buɗe wuta bayan ya sauko daga motar.
Ma’aikatan lafiya sun ce mutanen uku da aka kashe maza ne masu shekaru aƙalla 50, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Isra’ila suka ruwaito.
Isra’ila Ta Ce Za Ta Ci Gaba Da Kai Hare-hare A Gaza.
Musulman Najeriya Sun Daga Tutar Mauludin Annabi S A W.
Ƙungiyar Limamai A Najeriya Na Son Gwamnati Ta Gyara Matatun Mai Na Ƙasar.
Ƙasar Jordan ta ce ta ƙaddamar da bincike tare da rufe babbar gadar King Hussein, da ke mashigar Gaɓar Yamma, inda abun ya faru.
Lamarin ya faru ne a yankin da Isra’ila ke iko da shi, kuma nan ne motocin Jordan ɗauke da kaya ke bi don shiga Gaɓar Yamma.
Ko a cikin daren da ya gabata ma an samu musayar hare-haren makamai masu linzami tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Hezbolla ta Lebanon.
Ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon, ta ce ta harba makaman roka cikin arewacin Isra’ila, a matsayin martani kan harin Isra’ilar na ranar Asabar
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
-
Benue: Mutane 20 sun mutu, an ceto mutane 11 a hatsarin kwale-kwale.
-
Wasu mahara sun kashe Hakimi da kone gidaje a jihar Gombe.
-
Sojoji sun kama masu garkuwa da mutane tare da ƙwato alburusai a Filato.
-
Mun mayar da yara miliyan 1.5 makaranta a Borno – Zulum.