Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Jagoran jam’iyyar NNPP a jihar Bauchi ya fice daga cikin ta tare da dukka ƴaƴan jam’iyyar a jihar da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.
Sanata Halluru Jika wanda shine ya yi wa jam’iyyar NNPP a jihar Bauchi ta takarar gwamnan a zaɓen 2023 da ya gabat, ya koma APC ne a lokacin wani kwarya-kwaryan taro da shugaban jam’iyyar ta APC na Abdullahi Umar Ganduje jagoranta a ofishin jam’iyyar na kasa da ke Abuja.
Babban mai taimakawa shugaban jam’iyyar APC kan harkokin sadarwa na zamani Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana hakan a shafin sa na Facebook.
Yakasai ya ce Halluru Jika ya koma jam’iyyar ne tare da Ɗan takarar mataimakin gwamnan da ƴan takarar sanatoci guda 3, da na majalisar tarayya guda 12 da kuma ƴan takarar majalisar jiha su 31, da kuma shugabannin jam’iyyar gaba ɗaya suka shiga jam’iyar APCin a ƙarƙashin jagorancin shugaban jam’iyar NNPP na jihar Bauchi Alhaji Sani Shehu Sanin Mallam.
“Nan gaba kadan, Dr Ganduje zai jagoranci tawagar jam’iyyar ta kasa zuwa garin Bauchi domin ayi gagarumin bikin kona jar hula tare da karɓar duk waɗanda suka canja sheka tare da magoya bayan su, in ji shi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙungiyar LND ta su Shekarau za ta rikiɗe zuwa jam’iyyar siyasa.
-
PDP ta sha alwashin kwace mulkin Najeriya a hannun APC.
-
Sallamar da Gwamna Abba ya yi wa Sakataren Gwamnati da Kwamishinoninsa 5.
-
Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.
-
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.