December 2, 2021

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Ganduje Zai Cigaba Da Ginin Babbar Shelkwatar Ɗariƙar Ƙadiriyya Da Ke Abuja.

Page Visited: 1428
0 0
Read Time:43 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sha alwashin cigaba da ginawa mabiya Ɗarikar Ƙadiriyya babbar shelkwatar su gami da masallaci da ke Abuja  babban birnin tarayyar Najeriya wanda aka fara ginawa tun a shekarun baya.

Gwamna Ganduje, ya bayyana hakan ne a wajen taron maukibin Ƙadiriyya a aka yi ranar Asabar a birnin Kano wanda mataimakin sa Nasir Yusuf Gawuna, ya wakilta ya ce “insha Allahu kamar yadda gwamnan ya faɗa bayan an tashi daga wannan taro za’a nemi ƴan kwamiti kuma in Allah ya yarda za’a je a cigaba da gini na wannan katafariyar shelkwata saboda haka anyi tini a kan gaba”.

Ganduje yayi kira ga al’ummar jihar Kano su kara dagewa da addu’a domin kara samun zaman lafiya mai ɗorewa domin acewar sa “irin wadannan addu’o’i da bayin Allah sube ke yi sune suke kawo zaman lafiya”.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *