May 18, 2022

Gidauniyar Mai Tama Tugga Ta Nesanta Kanta Da Hannu Wajen Zaben Jam’iyyar APC A Jihar Bauchi.

Page Visited: 241
0 0
Read Time:40 Second

Daga Suleman Ibrahim Moddibo

Gidauniyar Mai Tama Tugga ta karyata rade-radin da ke yawo cewa gidauniyar na da hannu wajen daukar nauyin yin zaben shugaban jam’iyyar APC a jihar Bauchi.
Hakan na zuwa ne bayan bayan wani rade-radin da ke yawo kan cewa gidauniyar na da hannu dumu-dumu wajen shirya zaben.

Saboda haka ne gidauniyar ta karyata wannan batu, Abubakar Umar, shine sakataren watsa labarai na gidauniyar a jihar Bauchi ya ce, “ Gidauniyar Ambasada Yusuf Mai Tama Tugga, bata da halaka da zaben da aka yi, imma ya wuce cewa shi Ambasada dan jam`iyyar APC ne”.

“An zabi wanda yakamata a jihar Bauchi matsayin shugaban jam`yyar APC”.

A ranar Asabar 16 ga watan Oktoba ne dai jam`iyyar APC ta zabi Sunusi Aliyu Kunde a matsayin shugabanta na jihar Bauchi.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *