Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rahotanni a jihar Kano na cewa, an tabbatar da mutuwar mutum biyu, wasu biyu kuma sun tsallake rijiya da baya, a sakamakon rushewar wani bene mai hawa biyu a Jihar Kano.
Aminiya ta rawaito cewa, da misalin ƙarfe biyu a dare kafin wayewar garin ranar Alhamis ne benen ya rushe da su a unguwar Nomansland da ke Ƙaramar Hukumar Fagge.
Za A Samu Ambaliyar Ruwa A Kano Da Katsina da Zamfara Da Wasu Jihohin Arewacin Najeriya.
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi Ga Al’ummar Kiyawa.
Daga Ƙarshe Ɗan Ɗaban Da Ya Addabi Kano Abba Burakita Ya Mutu.
Benen ya rushe ne a sakamakon ambaliyar da ta biyo bayan ruwan sama kamar da baƙin kwarya na tsawon sa’o’i a cikin daren.
Kakakin hukumar kashe Gobara ta jihar Kano, Samun Abdullahi, ya ce an garzaya da waɗanda aka ceto daga bene da ya rushe zuwa asibiti, in da suke samun kulawa.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.