Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Zamfara, sun yi ƙoƙarin kashe wata Gobara wadda ta ɗauki lokaci tana ci a kasuwar Babura ta Yar Dole da ke birnin Gusau.
Wutar ta fara ci ne da yammacin ranar Asabar kuma shaguna da rumfuna da dama ne su ka ƙone.
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
Ƴansanda sun kama mutane 7 da ake zargin ƴan kungiyar asiri ne a Ogun.
Majiyarmu ta ce wutar ta bazu da sauri a cikin kasuwar, wacce ta ke wajen sayar da babura da kayan gyaransu a jihar.
“Ba mu san abin da ya jawo wutar ba. Mun dai ga hayaki daga shagunan babura, amma ma’aikatan kashe gobara na ƙoƙarin kashe ta.”
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.