An samu tashin gobara a ofishin Ƴansanda na a karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano da sanyin safiyar ranar Litinin dinnan.
kwamishinan Ƴansandan jihar, Hussaini Gumel,ya bayyana haka ga manema labarai inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 05:45 na safe inda wani gini ya kone gaba daya duk da cewa hukumar kashe gobara ta jihar ta kai dauki.
Gumel ya ce ana ci gaba da bincike don gano musabbabin tashin gobarar har zuwa wannan lokaci.
Yace an killace yankin domin hana kutsawar bata-gari, domin akwai makamai da alburusai da ke cikin ofishin wannan dalilin yasa aka rufe shige da fice a wajen.
A halin yanzu dai babban jami’in Ƴansanda na yankin yana kan tantance wasu takardun da abin ya shafa kamar yadda kwamishinan ya fada.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
An banka wa gidaje 24 da runbunan ajiyar hatsi wuta a jihar Jigawa bayan wani rikici ya ɓarke tsakanin Hausawa da Fulani.
-
Sojoji sun isa wasu ƙauyuka biyar a jihar Kebbi dan farwa Lakurawa, bayan sun kai harin da ya yi ajalin mutum 10.
-
Gwamantin Edo ta rushe gidan wani mutum saboda zarginsa da hannu a ayyukan garkuwa da mutane.
-
Gwamantin Kano ta ƙulla yarjejeniyar samar da sabbin motocin sufuri na zamani masu amfani da CNG.
-
Jam’iyyar PDP ta yi Alla wadai da dakatar da Sanata Natasha.