April 1, 2025

Gwamanti ta soke hawan Sallah a masarautar Bauchi

Yayin da wasu al’ummar musulmi ke shirin bukukuwan Sallah bayan kammala Azumi 29 ko 30 da shagalin hawan Sallah a masarautar Bauchi da ke jihar Bauchi a Arewacin Najeriya, Gwamnatin Jihar ta sanar da soke Hawan Sallar na bana.

Albarka Radio da ke Bauchi ta rawaito cewa, sanarwar soke hawan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban mashawarcin gwamnan jihar Bauchi a bangaren watsa labarai da Sadarwa Kwamared Mukhtar Gidado.

Sanarwar ta ce Gwamnatin Jihar Bauchi ta yi bayanin cewa daukar wannan mataki ya biyo bayan hukuncin da kwamitin kula da hawan masarautar Bauchi ya dauka ne na soke hawan ba tare da saka gwamnati a ciki ba, la’akari da tasirin hawan wajen nuna kyawawan al’adun Bauchi da ke jawo hankalin baki zuwa jihar.

Gwamnatin ta kuma ba da haƙuri ga jama’a sakamakon halin da za su samu kansu ciki sakamakon dalilin daukar wannan mataki.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *