Gwamnatin Jihar Kano ta kulla yarjejeniya da kamfanin Logistics Limited domin kaddamar da sabbin motocin sufuri na zamani, da ke amfani da iskar Gas, domin rage cunkoson ababen hawa a titunan Kano da saukaka zirga-zirga ga al’umma.
Da yake jawabi a wani taro da aka shirya domin sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) a ma’aikatar sufuri, Daraktan Kamfanin Stata Logistics Chuks Nwani, ya bayyana cewa shirin zai maye gurbin kananan motocin haya marasa tsari da dogayen motoci da ke amfani da Gas CNG, kowanne na daukar fasinjoji da kaso 120% fiye da motocin da ake amfani da su yanzu.
“Burina mu shi ne inganta harkar sufuri a Kano ta yadda zai zama mafi sauki, aminci, da araha ta amfani da motocin CNG. Wannan ba wai kawai zai rage kudin sufuri ba, har ma zai rage lokacin tafiya idan aka kwatanta da tsarin da ake da shi yanzu,” in ji Nwani.
A cikin wannan shiri, Stata Logistics za ta kawo motoci 135 na BRT da kuma gina tashoshin shan Gas CNG guda shidda a fadin jihar, domin tabbatar da wadataccen mai ga motocin. Kowacce mota ana kimanta ta da kudi dala $140,000 wanda jimillar jarin da za a zuba ya kai sama da dala $25 miliyan.
Nwani ya bukaci Gwamnatin Jihar Kano da ta samar da manufofi tsare-tsare da za su saukaka aiwatar da wannan shiri.
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano Ibrahim Ali Namadi ya yaba da shirin, yana mai cewa ya dace da kudurin sabuwar dokar Kano Metropolitan Agency (KAMATA) da aka sanya wa hannu kwanan nan, wacce ke da burin inganta sufuri a birane.
Ya bayyana kwarin gwiwa kan tasirin shirin, yana mai cewa Lagos ta zama misali na gyaran harkar sufuri a Najeriya.