March 12, 2025

Gwamantin Kano ta ware naira biliyan 8 domin shirin ciyarwar Ramadan.

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta ware Naira biliyan 8 domin shirin ciyarwar Ramadan na wannan shekara.

Gwamna Yusuf ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da rabon kwalayen dabino 1,250, da Masarautar Saudiyya ta bayar a matsayin gudunmawa, wanda aka gudanar a Fadar Gwamnatin Kano, a ranar Juma’a.

Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Tofa, ya fitar a ranar Assabar.

Gwamnan wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Alhaji Farouk Ibrahim ya wakilta, ya gode wa Jekadan Saudiyya a Kano Khalil Adamawi bisa wannan kyauta, ya na mai cewa wannan shi ne karo na hudu da Kano ke karɓar irin wannan gudunmawa.

Ya ce taimakon ya zo a daidai lokacin da gwamnati ke ƙoƙarin tallafa wa marassa galihu da kayan abinci, musamman duba da halin matsin tattalin arziki da al’ummar ƙasa ke ciki.

Yusuf ya bayyana Kano a matsayin jihar da ta fi zaman lafiya a Najeriya, lamarin da ya janyo mutane da dama suna kwararowa don zama a ciki, wanda hakan ke ƙara nauyi ga gwamnati, musamman a bangaren kiwon lafiya da gine-gine.

“Mai girma Jakada, a bana Ramadan ya zo a wani lokaci mai matuƙar wahala, yayin da Kano ke zaman ita kaɗai ce ta fi kwanciyar hankali a Arewa, hakan kuma ya sanya matsin lamba ga gwamnati akan jama’a, da kuma ababen more rayuwa,” in ji shi.

Gwamnan ya roƙi masarautar Saudiyya da ta gina asibitin masu tabin hankali da gyara sansanin yaran da suka rasa matsugunni a Kano, domin kyautata rayuwar waɗannan mutane.

Da yake magana Jakadan Saudiyya Ahmad Adamawi, ya jaddada cewa Saudiyya za ta ci gaba da bayar da tallafin jinƙai ga Gwamnatin Jihar Kano.

Ya yaba da manyan ayyukan da Gwamna Yusuf ke aiwatar wa a fannin lafiya, ilimi, da ababen more rayuwa a jihar.

A yayin taron, an raba dabinon ga ƙungiyoyin masu bukata ta musamman da wasu malaman addinin musulunci sauran su da dama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *