Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2024 inda yayi busharar faɗaɗa shirin gwamnatin sa na yaƙi da talauci da inganta ilimi, lafiya da kuma hanyoyi a yankunan karkara da birane.
Da yake jawabi yayi bikin sanya hannun da ya gudana a fadar gwamnati a gaban kakakin majalisar dokokin jiha da manyan jami’an gwamnati da shugabannin jam’iyyar PDP reshen jihar Bauchi, Bala Muhammad yace kasafin da ya ƙunshi sama da naira biliyan ɗari uku zai ɗora kan ayyukan waɗanda suka gabace shi na gina ɗakunan karatu a makarantin gwamnati, kwaskwarima wa manyan asibitoci tare da gina ƙanana a duk faɗin jiha.
Cikin sanarwa dauke da saka hannun Lawal Muazu Bauchi, Babban me tallafawa Gwamna Bala kan kafafen yaɗa labarai na zamani yace Gwamnan ya bayyana cewar sashen ilimi zai laƙume naira biliyan goma sha biyar, kaso me tsoka kamar yadda ya bayyana yayin taron inganta ilimi kuma wani matakin cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen sa.
Sai ya yabawa shugabancin majalisar dokoki kan goyon baya da haɗin kai da take bada fannin zartaswa inda ya ƙudiri aniyar ruɓanya shirin gwamnatin sa na damawa da kowa musamman mata da matasa da ya bayyana su a matsayin ƙashin bayan kowace al’uma.
Bala Muhammad sai ya godewa sarakuna da masarautun gargajiya, malaman addini da kuma ƙungiyoyi kan goyon bayan su ga jami’an tsaro a yaƙi da miyagu da ɓata-gari.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za a Fara Aikin Gyaran Dama-Daman Kano ta Kudu Nan ba da Jimawa ba – Gwamnatin tarayya.
-
Dokar haraji: Da sauran rina a kaba – Ali Ndume.
-
Za a fara shigar da kayan agaji Gaza gabanin yarjejeniyar tsagaita wuta ta soma aiki.
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.