January 31, 2023

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamna Bala ya sha alwashin inganta tsaro, yaƙi da talauci, yayi yaƙin neman zaɓe a Itas

Page Visited: 61
0 0
Read Time:50 Second

 

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Abdulƙadir Muhammad ya jaddada aniyar gwamnatin sa na cigaba da yaƙi da ayyukan ɓata-gari tare da faɗaɗa shirinta na yaƙi da talauci da zaman kashe wando tsakanin al’umar ta.

Muhammad ya bayyana hakan ne cikin jawaban sa ga al’umar Itas Gaɗau yayin gangamin yaƙin neman zaɓe karo na biyu inda ya bayyana shirin sa na cigaba da tallafawa rayuwar mazauna yankunan karkara.

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jam’iyyar PDP a jhar Bauchi ta samu nasarori da dama ciki har da ɗaga darajar sashen ilimi, lafiya, noma da kuma walwalar al’uma inda yace zai ruɓanya ƙoƙarin sa a zango na biyu.

Yayi amfani da damar wajen kira ga ƴan Najeriya da su zaɓi jam’iyyar PDP a dukkanin matakai don samun nagartaccen shugabanci.

A jawaban su daban daban, shugabanni da masu ruwa da tsaki daga yankin, yabawa gwamnan suka yi kan ayyukan raya ƙasa da ciyar da yankin gaba tare da ba shi tabbacin ƙuri’un su a zaɓe me zuwa.

Average Rating

5 Star
0%
4 Star
0%
3 Star
0%
2 Star
0%
1 Star
0%

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *