Majalisar Dokokin jihar Rivers ta gabatar da sanarwar zargin aikata ba dai-dai ba ga Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyar sa Farfesa Ngozi Odu, wanda ke nuna fara aiwatar da shirin tsige su.
Sanarwar da aka samo daga majalisar a ranar Litinin, ta bayyana cewa ‘yan majalisar sun ce wannan mataki ya yi dai-dai da kundin tsarin mulkin Najeriya.
Sanarwar ta ce wannan mataki “yayi dai-dai da tanadin Sashe na 188 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya na 1999 (wanda aka gyara) da sauran dokoki masu aiki.”
Sanarwar ta kara tabbatar da rade-radin cewa gwamnan na iya fuskantar tsigewa bayan hukuncin Kotun Koli, da ta amince da ‘yan majalisa 27 da ke biyayya ga tsohon gwamna Nyesom Wike, wanda ke takaddama da Fubara.
Wike wanda shi ne Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, ya kuma bayyana a makon da ya gabata yayin wata hira da manema labarai cewa, ya kamata a tsige Fubara idan an same shi da laifi.
“Siyasa ba wasa ba ce. Idan ya aikata abin da zai sa a tsige shi, to su tsige shi. Ba laifi ba ne,” in ji Wike.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƙudirin dokar da ke neman samar da Ofishin Firainista a matsayin Shugaban Gwamnati a Najeriya ya wuce karatu na 2 a majalisar wakilai.
-
Jami’an tsaro sun kama ɗalibai 59 a jihar Oyo
-
An dawo da ƴan Najeriya kusan 1000 gida daga ƙasar Libiya a farkon 2025 kawai
-
Masarautar Bauchi ta yi amai ta lashe kan soke hawan Sallah.
-
Kwastam ta kwace kuɗi kimanin naira biliyan 289 da aka boyi a katon ɗin yoghurt a Filin Jirgin Saman Abuja