January 7, 2025

Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.

Daga Sani Ibrahim Maitaya

Gwamnan jahar Borno da ke Arewacin Najeriya Babagana Umara Zulum, ya sanar da cewa gwamnatin jahar za ta saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boko Haram ya shafa.

Zulum ya sanar da saka tallafin ne a yammacin ranar Juma’a a garin Bama, lokacin da ya kaddamar da rabon kayan aikin gona ga manoma sama da dubu biyar da mayakan Boko Haram suka raba da muhallan su.

A cewar gwamnan, litar man fetur da ake sayarwa tsakanin naira dubu daya zuwa dubu daya da dari biyu a Maiduguri, za’a sayarwa manoma shi akan naira dari shidda.

Wannan dai na da nufin rage wa manoma matsalolin kudi da suke fuskanta a cikin al’ummomin da suka yi fama ta fuskar tattalin arziki da ababen more rayuwa a tsawon shekaru da aka kwashe ana rikici a yankin.

Sojan saman Nijeriya sun yi wa Ƴan Boko Haram fata-fata a Borno.

Tubabbun Ƴan Boko Haram 6,900 Sun Koma Cikin Al’umma A Borno

Sauyin Yanayi: Najeriya ta bayyana barnar da Ambaliyar ruwa ta yi a Borno da Zamfara a taron majalisar kasashen Afrika.

Zulum ya jaddada cewa irin wannan shiri da aka aiwatar a Damasak da ke karamar hukumar Mobar a shekarar da ta gabata, ya kara habbaka noman abinci da inganta rayuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *